Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wajibi ne Ekwerenmadu ya Ajiye Kayan da ba Nashi ba


Ginin majalisun tarayyar Najeriya
Ginin majalisun tarayyar Najeriya

Baya ga zaman da suke yi a majalisa wannan shine karo na farko da bangarori biyu na sanatocin jami’iyyar APC, zasu zauna a dakin taro tare domin su yin kokarin warware batun zaben shuwagabanin nasu. Saboda har yanzu ba’a zabe shugaban marasa rinjaye ba tukunna sai taro ya tashi baran baran.

Sanata Kabir Garba Marafa, yace ba nasaran da Saraki, ya samu shine yafi damun su ba yadda aka gudanar da zaben ne ya sabawa ka’idojin jami’iya.

Yana mai cewa “ Mun wayi gari mun shigo majalisa kawai sai mu kaga an zo da sabon littafi dauke da dokoki wanda ba’a bi tsarin yadda shi littafin yace ayi gyaran shi ba idan haka ta taso sabanin wanda muka saba amfani da shin a shekara ta 2011 zuwa 2015, ba’a canja shi ba tunda muka shigo damu aka yi majalisa kuma gwargwadon hali .”

Shima Suleiman Hunkuyi, yace “hanya daya ce kawai za’a bi kafin a samu masalaha, yana mai cewa “wajibi ne Ekwerenmadu ya ajiye kayan da ba nashi ba, ba aro bane in aro ne ma mai abin ya ga abinsa to a dawo masa dashi wannan shine gaskiyarmagana idan kuma bai yiba babu shakka mu dake da hakki amadadin iya jami’iyyar mu wa ‘yanda mun san kada daga ciki irin bakar wuyar da suka sha suka tura kansu zuwa inda suka kai a yanzu wajibi in ta kama mu kai maganar kotu zamu kai.”

XS
SM
MD
LG