Matasa a Shirye Suke Suyi Aiki da Hukumar INEC, 'Yan sanda a Zabe Me Zuwa

Wasu matasa masu kishin cigaban kasarsu Najeriya, suna kira da cewar yan’uwansu matasa da su mai da hankali wajen kawo kwanciyan hankali da zamanlafia a kasar.

Wasu matasa masu kishin cigaban kasarsu Najeriya, suna kira da cewar yan’uwansu matasa da su mai da hankali wajen kawo kwanciyan hankali da zamanlafia a kasar, ganin yada zaben kasar ke kara gurfanowa. Tabakin Mal. Yusuf Salisu Kofarwanbai, yace idan har gwamnati zatayi abubuwanta bisa adalci, to hakika za’a samu zabe nagartace, kuma yamakata ace su hukumomi suyi kokarin samar da abubuwan da suka kamata don gujema magudi da wasu tashin hankulla a lokacin zabe.

Wannan matashin dai, ya kuma yi nuni da cewar idan har gwamanti bazata yi amfani da hukumar zabe mai zamankanta ba da jami’an tsaro wajen muzgunama al’umah, to hakika za’ayi zabe nagari. Kasancewar abaya gwamnati na amfani da ‘yan sanda da sojoji wajen muzguna ma ‘yan kasa da barazana, wanda yake kaiwa da tauye hakin bil’adam.

Su dai wadannan matasan suna ganin idan har aka samar da shugabanci mai adalci to lallai za’a samu zaman lafia da kwanciyar hankali a lokacin zabe da ma bayan zabe. Kuma hakkin gwamnatine tayima al’uma adalci wajen fadin sakamakon zabe da ya dace. Sunce su abun da suka sani shine 'yan sanda abokan kowane, don haka suna kara kira da jami'an tsaro suyi aikin su yadda ya dace batare da wata tsangwama.