Matasa sun yi damara bayan sanya hannu akan kudirin da masu kula da al’amura ke ganin a matsayin wata zaburarrwa ga matasa wajen shiga hada-hadar siyasa domin bunkasa dimokradiyyar Najeriya.
Wani tsohon mataimakin shugaban babban bankin Najeriya kuma masanin tattalin arziki, Farfesa Kingsley Moghalu na neman Jam’iyyar YPP ta ba shi tikitin tsayawa takarar shugabancin Najeriya.
Ya bayyana manufofi da matakan da zai dauka domin tabbatar da hadin kai da kaunar juna tsakanin ‘yan Najeriya da kuma anniyarsa ta raya harkokin tattalin arziki, da ilimi a kasar.
Kwamarad Sani Yaro Kunya da ke zaman guda cikin wadanda suka shirya taron kuma babban mai tsare-tsaren Farfesa Moghalu a jihar Kano, ya ce yanzu lokaci ya yi ga matasa su nuna bajintarsu wajen ciyar da Najeriya gaba ta fuskar wanzar da shugabanci na gari.
Shugaban Jam’iyyar ta YPP reshen Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Sadauki Kabara cewa yayi, "Ni ba Moghalu kawai ba, duk mutumin da YPP ta tsayar cikin yardar Allah, domin dukkaninsu da ke neman mun fahimci cewa suna da nagarta. Kuma mun fahimci cewa jama'a sun gaji da halin da ake ciki," inji shi
Ya kuma ce suna sa ran za su ba wa Jam'iyyar APC kashi.
Your browser doesn’t support HTML5