A Jamhuriyar Nijar kungiyar masu sana’ar hannu da hadin guiwar abokan hulda na ketare sun shirya wani taron horo domin fadakar da matan jihohin kasar dubarun aikin fata ta yadda za a kara ingancin kayayakin da suke kerawa don ganin sun kara samin karbuwa a kasuwannin ketare.
An fara horar da rukunin farko na matan Nijar masu ayyukan hannu kan yadda za su koyi dabarun sarrafa fata wajen hada kayayyaki irinsu jakankuna da talakma.
Matan sun fito daga wasu jihohin Nijar hudu a tashin farko inda hukumomi suka bayyana cewa shirin wani yunkuri ne na karawa mata azama wajen fadi tashin da su ke yi wajen ganin sun dogaro da kansu.
“Matan da muka debo daga jihohi su ke, yanzu cikin kowace jiha an dauko mutum bi-biyu, sannan nan gaba ma za mu dauko mutum bi-biyu a sauran jihohin.” In ji shugaban kungiyar masu aikin hannu, Ibrahim Mousa.
Shirin horar da matan in ji shugabannin kasar wani yunkuri ne har ila yau na bai wa mata damar lakantar aiki da teloli masu aiki da wutar lantarki.
“Ana samun matsala, sai mutum ya baka aiki, mai dinki daban ma’aikaci daban, ana samun matsala.” A cewar mai horar da matan, Ibrahim Mai Kasuwa.
“Sana’a babu tabewa a cikinta kowacce iri ce, kiran da zan yi shi ne kamar idan an ba da horon a rika bi ana ganin yadda harkokin ke tafiya, tunda im ba kulawa babu ci gaba. In ji Malam Hauwa’u Mai Barma, wacce ta fito daga jihar Zinder daga cikin matan da ke samun horo.
Domin jin cikakken rahoton saurari wakilinmu Sule Mumuni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5