Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Wasu 'Yan Fashin Najeriya a Nijar


Mainasara Adili Toro, kakakin Rundunar 'Yan sandan Nijar
Mainasara Adili Toro, kakakin Rundunar 'Yan sandan Nijar

Matsalar tsaro akan iyakokin Najeriya da Nijar musamman ta fuskar dakile masu safarar makamai, na daga cikin matsalolin dake ci wa hukumomi tuwo a kwarya. Amma rahotannin daga Jamhuriyar ta Nijar na nuni da cewa a 'yan kwanakin nan jami’an tsaron kasar na samun galaba akan 'yan fashi da masu aikata miyagun laifuka.

Jami'an tsaro a Jamhuriyar Nijar na ci gaba da samun galaba a kasar, inda a kan iyakar garin Dan Issa a cikin jihar Maradi, aka yi nasarar kama wadansu 'yan Najeriya dauke da makaman yaki.

Rahotannin sun ce mutanen wadanda aka kama a cikin gundumar Dakwaro ta jihar Maradin sun yiwo fashi ne suna kan hanyarsu ta ficewa aka kama su.

"Batun tsaro ba gwamnati ce kadai ya kamata ta rika aiki ba, ya kamata 'yan kasa su rika ba da hadin kai wajen ba da labarai bisa kan abubuwan dake wakana." in ji Malam Hamza Garba, Magajin Garin Dan Issa, wanda ya tabbatar da aukuwa fashin.

A cewar sa, bayanan da mutane suka bayar ne suka taimaka a kama wadannan 'yan fashi.

"Wadannan mutane da aka kama dukkansu 'yan Najeriya ne wadanda suka samu wani dan kasuwa suka mai fashi, suna kuma kan hanyar komawa ne aka kama su." Magajin Garin ya kara ce.

Saurari cikakken rahoton Haruna Mamane Bako domin jin karin bayani:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00

Facebook Forum

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG