Tun lokacin da hare-haren Boko Haram suka tsananta a jihar Diffa hukumomi suka hana anfani da babura ko moto ta bakin 'yan Nijar.
Maharan suna anfani da baburan ne wajen kai hare-hare lamalarin da yanzu ya rage kimar babura wajen jama'a.
Kaka Aliyu mai sana'ar sayar da babura a jihar ta Diffa yace yau kusan shekaru biyu ke nan da babura basu da kasuwa saboda dokokin da aka kafa. Yace an kafa dokar ne sabili da Boko Haram domin suna yawan kai hare hare kan babura.
Masu sayen baburan yanzu ba 'yan jihar ba ne inji Kaka Aliyu. Wasu masu sayen suna zuwa ne daga Tawa ko Maradi ko Zinder. Haka ma 'yan kasuwa da sojoji da 'yansanda suna sayen baburan su tafi da su.
Hana hawan babura ya sa mafi yawan 'yan Diffa komawa ga hawan keke. Mustapha Idris wani mai sayar da kekuna yace kasuwar ta habaka. Mutanen jihar ma sun rungumi kaddara inda kowa yana hawan keke.
Ga rahoton Tamar Abari da karin bayani.
Facebook Forum