Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta yi kira ga kungiyoyin farar hula da kada suyi kasa a guiwa wajen mika rahotannin aikace-aikacen da suke yi a ko wace shekara.
Ministan ayyukan raya karkara Ammani Abdu, ne yayi wannan kira, lokacinda yake ganawa da wakilan kungiyoyin farar hula da suke aiki cikin kasar.
Ministan yace a cikin kungiyoyi fiye da dubu shida da suke aiki cikin kasar sama da metan 250 ne kadai suka gabatar rahotannin ayyukan da suke yi a shekara ta 2014.
Ya kara da cewa wannan umarni ya shafi dukkan kungiyoyin farar hula, walau na cikin gida ko kuma na kasashen ketare, wadanda suke aiki a Nijar din.
Ministan yace a bara kam ma, adadin kungiyoyin da suka gabatar da rahotanninsu sun yi baya, domin 180 cikin kungiyoyi fiye da dubu biyu ne kacal suka yi haka.
Yacce wannan hakki ne da ya wajaba akan kungiyoyin, kuma tilas su mutunta su.
Wani wanda yake da kungiyar farar hula a kasar, Alhaji Umaru Kado, ya yi kira ga gwamnatin Nijar ta tashi tsaye wajen ganin ta san ayyukan da irin wadannan kungiyoyi musamman na ketare harda na cikin gidan suke aikatawa, da hanyoyin a suke samun kudi da kuma burorinsu.
Facebook Forum