A sanarwar da ta fitar da sanyin safiyar Laraba 25 ga watan Afrilun 2023 wacce aka aike wa manema labarai, ma’aikatar ministan harkokin wajen jamhuriyar Nijar ta bayyana farin ciki akan abinda ta kira samun nasarar kwashe jami’anta daga Sudan su kimanin 38 da suka tsallaka kasar Djibouti da taimakon dakaru na musamman da ake kira Forces Speciales na kasar Faransa.
Gwamnatin Nijar ce ta tuntubi ofisoshin jakadancin Faransa a Khartoum da Yamai akan bukatar bai wa wadannan jami’ai damar shiga ayarin ‘yan Faransa da aka kwashe daga Khartoum a cewar sanarwar.
Shugaban kungiyar Voix des sans Voix Nassirou Saidou, da ke bayyana ra’ayinsa, ya yaba da wannan mataki da ya ke kallo a matsayin wata alama ta kyakkyawar huldar kasashen biyu.
Ko da yake babu wasu alkaluma na hakika a hukumance dangane da yawan ‘yan Nijar mazauna Sudan, wasu majiyoyi na kwatanta cewa miliyoyi ne ke rayuwa a wannan kasa ta yankin gabashin Afrika haka kuma akwai dalibai ‘yan Nijar da ke karatu a jami’o’in Sudan, abinda ya sa shugaban kungiyar Kulawa da Rayuwa Hamidou Sidi Fody, ke nuna damuwa a kan halin maraicin da aka bar wadannan bayin Allah a ciki bayan da aka kwashe jami’an jakadancin Nijar daga Khartoum.
Wannan ya sa Saidou ke shawartar gwamnatin Nijar da ta dage da neman hanyoyin kubutar da sauran ‘yan kasar daga halin tsaka mai wuyar da ake ciki a Khartoum.
A hirar da Muryar Amurka ta yi ta waya da su a yammacin Litinin, dalibai ‘yan Nijar da ke Sudan sun koka a game da abinda suka kira halin ko in kula da jami’an karamin ofishin jakadancin kasar suka nuna a game da halin da suke ciki, akwai lokacin da abinci, da ruwa, da wutar lantarki suka yi wuya sakamakon kazamin fadan da aka shafe kwanaki sama da 10 ana kafsawa a tsakanin janar-janar din da ke hamayyar rike madafun iko.
Saurari rahoton Souley Mumuni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5