Bayan Mali da Burkina Faso ne mataimakin Firai Ministan Rasha Alexandre Novak ya sauka birnin Yamai a karshen mako inda ya gana da hukumomin kasar.
"Yace mun yi tattaunawa mai armashi da shugaban majalisar CNSP da Firai Minista Lamine Zeine. Shugaba Putin ya ba da umurni a karfafa hulda da kasashen Afirka musamman mambobin kawancen AES. Nijar na daga cikin dadaddun kasashe kawayen Rasha wadanda huldarsu ke tasiri sosai kan tafiyar duniya. A yanzu mun shiga ayyukan sake bude ofishin jakadancin Rasha a Nijar, mun kuma yi magana akan ayyukan da ka iya shafar ‘yan kasuwar Rasha a fannin makamashi, sufuri, noma da ma’adanai. Dukkanmu mun amince mu fara wadanan ayyukan idan so samu ne nan ba da dadewa ba," a cewar Novak.
A fadar Fira Minista tawagar ta Rasha ta gana da jami’an gwamnati da ‘yan kasuwar Nijar akan batutuwan da suka shafi harkokin kasuwanci a tsakanin kasashen biyu da ma batun saka hannun jari. Chaibou Tchombiano, na daga cikin shugabannin ‘yan kasuwar Import Export da suka halarci wannan zama, ya ce yana fata Rasha za ta taimaka musu don su bunkasa kasuwancinsu ta fannanonin noma, kasuwanci, ma’adinai da sauransu.
A kan batun tsaro jami’an kasashen biyu, a karkashin jagorancin ministan tsaron Nijar Janar Salifou Mody da takwaran aikinsa Yunus Bek Yevkurov, sun jagoranci zama kan inganta huldar tsaro, fannin da ke kara kusantar da gwamnatin Moscow da hukumomin Nijar tun bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin 2023. Masani kan sha’anin tsaro Abass Moumouni na hasashen yiwuwar Nijer za ta mori wannan alaka.
"A kullum Rasha na tinkaho da cewa ba ta taba yi wa wata kasa mulkin mallaka ba, tana alaka da kasashe ne a matsayin kasa-da-kasa, hakan na nufin Nijar za ta mori wannan kawance," a cewar Moumouni.
Rangadin mataimakin Firai Ministan na Rasha ya wakana ne a daidai lokacin da kasashen Afirka ke kara kwance ragowar igiyoyin mulkin mallaka daga wuyansu, inda a baya-bayan nan cikin yanayin bazata Chadi ta sanar da kawo karshen huldar tsaro da Faransa mai sansanin soja sama da 1,000 a birnin N’djamena, yayin da shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye, ya bayyana fatan ganin Faransa ta rufe sansanoni biyu da ta ke da su a kasarsa domin abin da ya kira tabbatuwar cikakken ‘yanci kan kasa.
Saurari cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5