Mata 'Yan Kasa da Shekaru Ashirin na Rawa Tsirara a Wata Mashaya

‘Yan sintiri a jahar Delta, a Najeriya, sun gano wata mashaya a garin Asaba, inda ake anfani ‘yan mata ‘yan kasa da shekaru ashirin a mashayar a matsayin masu rawa inda kuma suke rawar tsirara.

Shugaban ‘yan sintirin Chukudi Nnamdi, wanda ya tabbatar da kama mai gudanar da wannan aikin masha’a yace tuni aka mika shi ga hukumar ‘yan sandan jahar ta Delta.

Bincike ya nuna cewa mashayar inda ake gudanarda wannan masha’a ya kan kasance a cike makil da jama’a masamman a karshen mako, kuma akasarin ‘yan mata kan zo ne daga makwabtan jahohi.

Daya daga cikin ‘yan mata dake wannan harka mai suna Ogechi, tace suna samun kudi a duk lokacin da suka halarci mashayar daga Naira dubu ashirin zuwa Naira dubu ashirin da biyar, ta kuma ce ‘yan sanda basu taba tsangwamarsu ba.

Hukumar ‘yan sandan jahar ta Delta, ta bada tabbacin cewa a yanzu haka mai wannan mashaya yana hannu.