Kasar Masar ta fitar da kanta daga wasannin kwallon kafar maza da mata na kasashen Afirka na wannan shekarar ta 2015, wanda aka shirya yinsu a Congo, cikin wata mai zuwa.
Hukumar kwallon kafa ta kasashen Afirka (CAF) ta tabbatar da wannan hukunci da kasar Masar ta yanke, amma ba’a fitar da dalilin yin hakan ba.
An dai shirya cewa Masar din zata gamu da Najeriya da Ghana da Senegal a cikin rukuninsu na B a wasan maza, a bangaren Mata kuwa su zasu hadu da kasar Kamaru da Ghana da Afirka ta Kudu.
Hukumar CAF dai zata maye guraben kungiyoyin biyu, na maza da kasar Burundi, na mata kuwa da kasar Senegal. Hukumar CAF ta yi amfani ne da wani bangare na tsarin dokarta, sashe na 19, wanda ya bayyana cewa idan har kungiyar wasa ta fitar da kanta bayan da sami shiga gasar wasa, to kwamitin hukumar zai maye gurbin ta da wadda kungiyar ta fitar a karshe.
Gasar wasannin dai na kasashen Afirka an shirya yinsu 6 zuwa 18 ga wata mai zuwa na Satumba.