Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fasahar Android One Ta Kamfanin Google Ta Kai Najeriya


Kamfanin Google ya fitar da wata sabuwar fasaha ta kera wayoyin hannu mai Kyau da rahusa da arha da karko, a Najeriya da sauran wasu kasashen Afirka biyar, ta cikin wani shiri mai suna Android One Program. Shirin dai ya fara ta amfani da wayar Infinix HOT 2-X510 a Najeriya.

A wani taro da Google tayi a Najeriya wanda ya janyo hankalin mutane sosai a jihar Lagos, Google ya dai bayyana cewa cikin ‘yan makonni masu zuwa mutane zasu iya kallon hotunan bidiyo na Youtube ta wayoyin su ba tare da yin amfani da datar su ba, a kasashen da suka hada da Najeriya da Masar da Ghana da Kenya da Morocco, hakan zai baiwa mutane damar ajiye hotunan bidiyo na Youtube, kuma duk lokacin da suka kashe datar su zasu iya kallon bidiyon batare da amfani da datar su ba.

Bisa ga masu kiran kasuwar wannan shiri sunce wannan wani kudirine na tabbatar da cewa an samar da wayoyin hannu masu dauke da fasahar zamani ga miliyoyin mutanen dake nahiyar Asiya da Afirka dama sauran kasashen duniya.

Kamar yadda Caesar Sengupta wani babban jami’in Google yace, “Sama da mutane biliyan uku dake fadin duniyar nan na amfani da yanar gizo domin samun ingantacciyar rayuwa, dama kirkirar dama ga duk al’umma.

Ya ci gaba da cewa samar da wannan wayar ga Najeriya da sauran kasashen Afirka abu ne mai kyau, idan aka duba kashi 70 cikin dari a Najeriya na amfani da wayoyin su domin wajen shiga internet. Android One zata basu duk abinda suke so, kuma cikin rahusa.

Infinix HOT 2-X510 itace wayar farko da dake da fasahar Android One da aka fitar a Afirka, yanzu haka za’a iya sayan wannan waya akan shafukan yanar gizo cikin sauki.

XS
SM
MD
LG