Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yanke Mata Hukuncin Kisa Akan Hodar Iblis


Ranar alhamis da ta gabata wata Kotu ta yanke ma wata mata mai shekaru talatin da haihuwa Chomanee Laphathanawat, daga lardin Rayong hukucin kisa bayan an same ta da laifin safarar hodar ibilis mai nauyin giram 689.10 wadda aka zuzzuba ta cikin nau’in kwayoyin kafso sa’annan aka boye su duka a cikin dubura da kuma gaban ta.

A cewar rahoton Malaymail, an kama matar ne a filin jiragen Penang a birnin Bayan Lepas a cikin watan fabarairun da ya gabata.

A cewar Chonmanee, ta nemi taimakon ‘yan sandan filin jirginne a yayin da ta ji zafi daga kasan marrar ta kamar zai hallaka ta.

Ta kara da cewa wasu mutane ne a Brazil suka tilasta mata hadiye kwayoyin da kuma sa wasu a cikin gaban ta da kuma duburar ta.

A ta bakin jami’in da kotu ta sa domin wakiltar matar, ya bayyana ma kotun cewar matar bata da masaniya akan cewar hodar ibilis ce a cikin kwayoyin kafson.

An bayyana cewa tun daga tasowar jirgin daga Brazil zuwa Malaysia inda suka yada zango a Barcelona, da Spain da Singapore, yawan baccin da matafiyar ta yi ya nuna cewar tana cikin wani mawuyacin hali na rashin lafiya.

A cewar mataimakin mai yanke shari’a Amir Hamdzah Othman, y ace matar ta kasa bada wata shaidar da zata kare ta daga abubuwan da ta fadi wa kotun, ya kuma kara da cewar babu makawa akan cancantar hukucin da aka yanke mata.

Ya kara da cewa matar bata fada wa hukumomin Barcelona ko Spain a lokacin da suka yada zango kafin isar su garin Penang ba.

A cewar sa “ai da ta duba ta ga menene ke cikin kafson da aka boye a gabanta. matsalar da ta sa kanta ta rashin kula bazata ta taba kubutar da it aba.

Othman ya kara da cewa, “na gamsu da irin hukuncin da aka yanke mata”

Daga karshe, mai shari’a Nordin Hassan ce ta yanke wa matar hukuncin kisa a sakamakon samun ta da laifi dumu dumu.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG