Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wutar Lantarki Ta Tona Musu Asiri


‘Yan Sanda a jihar Pennsylvania, ta kasar Amurka sun gano wani mutun da budurwarsa a kwance suna barci a garejin mota, a gidan wata mata bayan da suka shiga gidan batare da izini ba.

‘Yan Sandan sun gano mutanen ne bayan da mai gidan ta kai rahoton cewa an shiga mata gida, kuma asusun ta da take ajiya a ciki ya bace, sannan kuma an yi mata bincike dan ta samu gidan a hargitse.

Ta kara da cewa ta samu akwatin kudin ta a bayan gidan ta sa’ilin nan jakar ta ma ya bace sannan kofar gidan a balle.

‘Yan Sandan sun ce wutar lantarkin garejin motar da aka bari a kunne ya taimaka wajen gano su.

Mutumin mai suna Spencer Peak, za’a fara sauraran kara sa ranar 1, ga watan Satumba, amma budurwasa ba zata gurfana a gaban Kotu ba.

XS
SM
MD
LG