Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce wadanda ke yi wa gwamnatinsa zagon kasa domin a ga gazarwarta ba za su yi nasara ba.
Buhari ya bayyana hakan ne a jawabin da ya yi wa 'yan kasar yana mai nuni ga wadanda suka haddasa matsalar karancin man fetir a kasar, lamarin da ya jefa al’umar Najeriya cikin mawuyacin hali.
“Irin wannan rashin kishin kasa ba zai kawar da akalar muradun da muke so mu cimma ba.” Buhari ya fada a jawabin nasa wanda aka watsa ta kafar talbijin.
Shugaban na Najeriya ya kuma ce sai inda karfinsa ya kare wajen zakulo wadanda suka hada kai suka gallaza wa ‘yan Najeriya.
“Za mu tabbatar da cewa wadanda ke da hanu a wannan lamari an zakulo su an kuma dakile sake aukuwar hakan.” Shugaban ya ce.
Baya ga batun matsalar karancin man fetir, Buhari ya kuma tabo batutuwan da suka shafi yadda gwamnatinsa ta kuduri aniyar kammala ayyukan layin dogo da za su hada sassan kasar.
Sannan Buhari ya yi magana kan batun ayyukan manyan hanyoyin kasar guda 25, wadanda ya ce gwamnatinsa ta sa su a gaba domin ganin an kammala su.
Buhari wanda mulkinsa ya doshi shekaru uku, ya kuma tabo batun ayyukan wutar lantarki da ya ce ana samun ci gaba.
“Yawan adadin wutar lantarki ya kai Megawatts 7,000. A ranar 8 ga watan Disamba 2017, mun samu nasarar raba wutar lantarki megawatts 5,155 ga masu amfani da wutar ta lantarki, wanda shi ne adadi mafi yawa da muka taba samu.”
Har ila yau shugaban na Najeriya wanda ke mulkin karkashin jam'iyar APC, ya tabo batutuwan noma da tsaro da kuma yanayin siyasar kasar.
Saurari rahoton Nasiru Adamu El Hikaya domin karin bayani:
Your browser doesn’t support HTML5