Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci Gaba Da Yi wa Buhari Jajen Hatsarin Da Dansa Ya Yi


Yusuf Buhari
Yusuf Buhari

Ana ci gaba da yi ma Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari jaje da fatan alheri bayan hatsarin da dansa ya yi da mashin. Tuni malamai da talakawan Najeriya suka shiga addu'o'i da kuma bayyana fatan alheri da aikewa da sakonnin karfafa kwarin gwiwa ga Shugaban kasa da iyalinsa.

‘Yan Najeriya na ci gaba da yi wa Yusuf, dan Shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’a bayan hadarin mashin da ya janyo masa raunuka a kai da kuma karaya.

Fadar shugaban kasra ta fitar da sanarwar cewa yana karbar magani a wani asibiti da ke Abuja inda aka yi masa aiki har da kansa.

Da ya ke tabbatar da aukuwar lamarin ga wakiliyar Sashin Hausa Madina Dauda, babban jami’i mai magana da yawun Fadar Shugaban Najeriya Garba Shehu, ya ce tun bayan da aka yi ma Yusuf Buhari aiki sanadiyyar hatsarin yake samun sauki.

Shehu ya ce Shugaba Buhari da maidakinsa sun je asibitin sun ga Yusuf.

Ya ce shugaba Buhari da sauran dangi na gode ma ‘yan Najeriya saboda addu’o’in da su ke yi.

Ga Madina Dauda da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG