NIAMEY, NIGER - Wannan ya sa masana sha’anin tsaro suka fara jan hankulan mahukunta a kasashen Sahel akan maganar hadin kai.
Sun kara da cewa wannan al’amari manuniya ce ga sojojin juyin mulkin Nijar da su bi hanyoyin warware rikicin da ke tsakaninsu da Faransa cikin ruwan sanyi kamar yadda mai sharhi akan sha’anin tsaro Abdourahaman Alkassoum ya bayyana mana a wata hirar.
Rashin girke dakaru a yankuna da dama na Arewacin Mali ya sa kungiyar IS kara yada manufofinta da samun iko da wurare da dama a wani lokacin da ‘yan tawayen Abzinawa ke kara kafuwa yayin da kungiyar JNIM ke kara dannawa zuwa yankin kudancin kasar a cewar Abdourahaman Alkassoum.
Sai dai ya kara da cewa, za a iya canza abubuwa da zarar kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar sun hada kai domin yakar ‘yan ta’addan da suka addabi yankin na Sahel kasancewar a halin yanzu akwai fahimta a tsakanin kasashen uku da ke karkashin mulkin soja.
Mai sharhin ya kuma yi gargadi ga sojojin da suka kifar da gwamnatin farar hula ta Nijar da ta bi hanyyoyin sulhu don su rabu lafiya da Faransa wacce yake ganin gwabza yaki da ita ba zai samar wa Nijar da wata nasara ba.
Saurari yadda hirar ta su ta kaya da wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5