Yadda Masu Goyon Bayan Juyin Mulki Suka Kai Hari Ofishin Jami'yyar PNDS Mai Mulki A Nijar

Akwai Sauran Hadari A Nijar - Masu Sharhi

Wasu masu zanga-zangar goyon bayan sojojin da suka yi juyin mulki a kasar sun yi kaca-kaca da ofishin jam’iyar PNDS mai mulki a yau Alhamis tare da kwasar ganima da farfarsa gilasai da kona gomman motoci.

NIAMEY, NIGER - Daruruwan mazauna birnin Yamai ne suka taru a dandalin Place de la Conceration inda suka gudanar da gangamin goyon bayan sojojin kwamitin CNSP wadanda suka bada sanarwar kifar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum. Suna masu nuna farin ciki da wannan juyin mulki kamar yadda daya daga cikinsu Gamatche Mahamadou y shaida wa Muryar Amurka.

Nijar

Masu zanga-zangar sun fantsama titunan birnin Yamai inda a karshe suka nufi ofishin jam’iyar PNDS Tarayya a daidai lokacin da wasu kusoshin jam’iyar ke gudanar da taro. Isar su ke da wuya suka afka cikin ofishin jam’iyar dake n’guwar Zabarkan inda suka kwashi ganima kafin su ka cinna wuta yayin da wasu daga cikinsu suka farfasa gilasai tare da kona motocin da aka kyasta cewa sun kai 30.

Nijar

Masu sharhi akan al’amuran yau da kullum na cewa har yanzu da sauran hazo a halin da aka shiga a kasar ta Nijar duk da cewa soja sun tabbatar da kifar da gwamnati.

Kawo zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a bayyana sunan wanda zai Shugabancin kwamitin CNSP na sojojin da suka kifar da gwamnati ba haka kuma ba wani bayani dangane da abinda ke tafe da tawwagar kungiyar ECOWAS a nan birnin na Yamai.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Masu Sharhi Akan Al’amuram Yau Da Kullum Sun Ce Akwai Saruan Hadari A Nijar.mp3