Kampanin Yahoo ya fada jiya Alhamis cewa masu kutse a yanar gizo sun saci bayanan mutane a kalla miliyon 500 masu amfani da shafin duniyar gizo na Yahoo.com.
WASHINGTON, DC —
Kampanin na Yahoo yace binciken da ya gudanar ya nuna cewa wannan kutsen na da nasaba da abin da yake ganin wasu masu samun tallafi daga kasashen wajen Amurka ne ke wannan aiki.
Kampanin yace an saci bayanan wasu masu amfani da shafin, sai dai bai yi Karin bayani ba a kan adadin masu amfani da sahfin nasu da wannan kutse zai shafa ba.
Duk da haka ana kyautata zaton cewa watakila barayin bayanan sun yi awon gaba da bugun sunaye, da adireshin email da lambobin waya, da ranakun haifuwa da alamomin sirri (password) na jama’a masu yawa. Amma kampanin ya kuma ce wannan kutsen bai shafi lambobin sirri masu kariya da takardun biyan kudi na banki da bayanan banki.