Tuni dai ‘Yan adawa suka zargi gwamnatin Syria akan wadannan hare-haren, duk da dai jami’an gwamnatin basu ce komai akai ba. Bayan wadannan hare-hare ne kuma kazamin fada ya barke a garin an Aleppo.
Harin Jiragen saman ya kashe kimanin fararen hula 12, wanda hakan ya janwo matsalar karya alkawarin tsagaita wutar
da Amurka da Rusha suka kulla a matsayin masu shiga tsakani tun a farkon wannan watan.
Kerry yace idan dai har ana son yarjejeniyar tsagaita wutar da ke tangal-tangal ta dore, to lallai sai an dakatar da kai hare-hare da jiragen yaki. Musamman a wuraren da kungiyoyin agaji ke kokarin kai abinci da magunguna.
Kerry ya mika kukansa a babban taron Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, inda ya bayyana bukatar kayyade tashin jiragen yakin, da cewa yana da matukar muhimmanci don kawo karshe zubar da jini a Syria.