Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Jihar North Carolina Ta Amurka Ya Kafa Dokar TA Baci


'Yansanda sun yi taho mu gama da masu zanga zanga
'Yansanda sun yi taho mu gama da masu zanga zanga

Gwamnan jihar North Carolina (Karolaina) ya tabbatar da kafa dokar ta baci a birnin Charlotte, tare da kai Jami’an tsaro na kasa wato National Guards cikin birnin.

A daren jiya aka fara zanzangar lumana, wacce ta rikide zuwa rikice-rikece tsakanin ‘yan sandan kwantar da tarzoma da masu zanga zangar. Har hakan ta sa ‘yan sanda harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa su. Wasu mutane sun farfasa tagogin shaguna gami da kunna wuta a kan hanyoyi.

Gwamnatin birnin ta bayyana cewar wani mutum ya rasa ransa sakamon harbinsa da wani farar hula yayi, daga baya kuma aka ce wannan mutum ya ji mummunan rauni ne. ‘Yan sandan garin Charlotte sun bayyana cewar jami’ansu hudu ne suka dan jij-ji rauni.

Masu zanga zanga
Masu zanga zanga

Zanga zangar ta faru ne sakamakon harbin wani mutum mai suna Keith Lamont Scott dan shekara 43 a wani gida, wanda ‘yan sanda suka ce suna neman wani ne daban yayin da shi Scott, ya fito daga cikin mota da bindiga, shi kuma jami’in Dan sandan ya harbe shine sakamakon kin ajiye bindigar da yayi.

XS
SM
MD
LG