Wannan sabon maganin Zika da masu nazari a cibiyar kiwon lafiya ta kasar Amurka suka gwada kuma yana aiki, ya zama wani sabon nau’in magani ne wanda ke amfani da fasahar kwayar halitta ya karfafa garkuwan jikin mutum ta yadda zai iya yakar cutar.
Sakamakon yanda cutar Zika ke gaggauta yaduwa, nan bada dadewa ba za’a jarraba wannan magani. Izuwa yanzu ba a bada izinin jarraba wannan magani a kan bil adama ba a nan Amurka, amma dai dakin gwaji na Graham na kokarin kayyade yawan maganin da za’a rinka sha don samun cikakken kariya.