Ana sa ran wannan yarjejeniya r ta taimaka wajen magance matsalolin tsaro da kasar da yaki ya daidaita, da kuma fatan wannan zai baiwa sauran kungiyoyin tsageru karfin gwiwar kulla irin wannan shiri.
Wannan itace yarjejeniya ta farko cikin shekaru goma sha biyar tun da yan Taliban suka fara yaki a kasar. Bayan Dakarun Hadin gwuiwa na Amurka suka tsige su daga kan mulki.
Kungiyar Mai suna Hizb-Islami tana karkashin jagorancin Gulbuddin Hekmtyar kwamandan da ya dade yana yakin sunkuru inda mayakan sa ada suka yaki tshohuwar tarayyar rasha a shekarar 1980, daga baya kuma suka yaki yan Taliban kan jagorancin Afghanistan a mummunan yakin basasar da akayi a 1990.
Hanif Atmar Mai bada shawara kan harkokin tsaro ne ya rattaba hannu akan yarjejeniyar tare da wakilin Hekmatyar, Karim Amin a taron da aka nuna kafafen yada labarai.
Wannan sasan tawa zata baiwa mai gujewa dokar damar dawowa cikin siyasar kasar bayan shekaru da ya kwashe ana has ashen yana boye a bangern Pakistan.
Bayan babu wata matsala da aka fuskanta wajen yarjejeniyar zaman lafiyan, masu fafutukar hakkin dan adam sun hau tituna suna allah wadai da Hekmatyar da irin ta’asar da ya aikata a baya.