Kalaman ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike na mayar da birnin kan taswirarta na asali, ya kunshi kwace filayen da gwamnati ta bayar da masu shi basu yi aiki a kai ba a tsawon lokaci, rushe gine-ginen da aka yi ba bisa ka’ida ba, haramta yin kananan sana’o’i a kan tituna da dai sauransu. Lamarin da wasu su ka yi marhaba da kalaman nasa, yayin da wasu kuma su ka kushe kalaman.
Tun bayan da aka mayar da Abuja, babban birnin Tarayyar Najeriya, a shekarar 1991 daga tsohon babban birnin kasar wato Legas ne aka fara ganin kwararowar al’umma daga sassan kasar daban-daban don aiki, kasuwanci, cinikayya da dai sauransu baya ga cudanya da ‘yan asalin birnin wadanda ke zaune a ciki tun kaka da kakanin.
A wancan lokacin a cikin aikin bunkasa sabon babban birnin kasar, an tsara babbar taswira a cikin shekarar 1979, kuma aka fara aiwatar da ayyukan ci gaba, sai dai tun bayan lokacin ne yawan al’ummar Abuja ta ci gaba da karuwa bisa yawan karuwar al’ummar kasar baki daya, kuma ana hasashen za su kai miliyan 11 nan da shekarar 2035.
To sai dai masana sun ce daga bisani mahukunta masu gudanar da babban birnin da suka biyo baya a Abuja sun katse ci gaba da amfani da taswirar asalin lamarin da ake ganin shi ya jefa talakawa mazauna birni komawa wajen gari da kansu kuma hakan ya haifar da ƙauyuka mara tsari a kewaye da birnin.
Za’a iya cewa farfado da batun komawa kan asalin tsarin taswirar birnin tarayya Abuja da sabon Minista Nyesom Wike ya yi ya bar baya da kura kamar yadda wasu masu kananan sana’o’i dake fitowa daga wajen gari suna zuwa gashin masara, sayar da kati, tukin keke naped da dai sauransu bayyana, inda wasu suka bukaci a samar musu da mafita idan za’a tada su daga cikin gari.
Kazalika jiga-jigan ‘yan siyasa, masu fada a ji, lauyoyi dai sun yi ta jan hankalin Wike da ya bi abubuwa sannu a hankali kan abun da suke kallo kamar barazanar yin rusau a birnin Abuja, inda suka caccaki barazanar yin rusau da sabon ministan ya yi a shafukansu na sada zumunta bayan an rantsar da shi a ranar Litinin, 21 ga watan Agusta.
Wike dai ya sha alwashin tsaftace birnin Abuja da kuma rushe duk gine-ginen da ke ba bisa ka'ida ba, ko na wanene kuwa, baya ga batun hana yawo da dabobbi, korar masu kananan sana’a a kan tutina da dai saurasu.
Kwararre a fannin tsara Birane kuma dan asalin yankin Abaji na birnin tarayya Abuja, TPL Abubakar Sadik Ahmad, yace ba wani sabon abu bane Minista ya ce zai koma asalin taswirar tsara birnin Abuja ganin yadda haka abun yake a dokar tsara birane.
Idan Ana iya tunawa, birnin Abuja dai ya sami Ministoci kamar Mobolaji Ajose-Adeogun a shekarar 1976 zuwa 1979, John Jatau Kadiya daga shekarar 1979 zuwa 1982, zuwa Mal. Nasir Ahmad El-Rufai a shekarar 2003 zuwa watan Mayun shekarar 2007 da masana ke kallon ya yi aiki tukuru wajen sauya fasalin birnin zuwa daya daga cikin manyan birane a nahiyar Afrika.
Saurari cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5