Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sanya Wasu Tsoffin Gwamnoni A Jerin Ministocin Shugaba Tinubu Ya Jawo Cece-Ku-ce Tsakanin 'Yan Najeriya


Shugaba Tinubu
Shugaba Tinubu

Shugaba Tinubu ya aike da sunayen jimlar tsoffin gwamnoni tara zuwa majalisar tarayya domin tantance su, wani abu da ya jawo cece-ku-ce a tsakanin 'yan Najeriya duba cewa wasu daga cikinsu basu tabuka abin a zo a gani ba a jihohinsu.

A ranar Laraba ne Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya aike wa Majalisar Tarayyar kasar da rukuni na biyu na jerin sunayen wadanda za a tantance domin basu mukaman Ministoci, daga cikin jerin sunayen akwai tsoffin gwamnoni tara, da suka hada da Nyesom Wike daga Jihar Rivers, Ibrahim Geidam daga yobe, Nasir El-Rufai daga Kaduna, Mohammed Badaru daga Jigawa, Atiku Bagudu daga Kebbi, Bello Matawalle daga Zamfara, Simon Lalong daga Filato, Adeboyega Oyetola daga Osun, da kuma David Umahi daga Jihar Ebonyi.

'Yan Najeriya sun bayyana mamakin ganin tsoffin gwamnonin a cikin wadanda za a bai wa mukaman Minista, duk da cewa basu tabuka abin azo a gani ba a lokacin da suke gwamnoni a jihohinsu, wasu kuma ana zarginsu da cin hanci da rashawa.

Hon. Abubakar Adamu Musa, shi ne sakataren tsare-tsare na jam'iyyar APC a arewa maso gabashin Najeriya, yace hakan ya zamo tilas ne ga Shugaba Tinubu ya surka da tsoffin gwamnonin saboda karfin tasirinsu. Ya kara da cewa a siyasar Najeriya babu rukunin da ya fi karfi kamar na gwamnoni.

Sai dai Comrade Sa'idu Bello, wanda shi ne kodinatan Atiku Forum, yace sanya tsoffin gwamnonin a jerin sunayen Ministocin da za a nada "Zani ce ta tadda muje," domin hakan ya nuna cewa sam Shugaba Tinubu bai shirya gyara ire-iren kura-kuran da jam'iyyar APC tayi a baya ba.

Dr. Faruq Bibi Faruq, manazarci kan harkokin siyasa da dimokradiyya daga jami'ar Abuja, yace bai wa tsoffin gwamnoni mukaman Minista "rama wa kura aniyarta ne." Ya kara da cewa sun dai shigo gwamnati ne don a raba jarin gwamnati da su saboda rawar da suka taka a lokacin neman zabe.

Yanzu dai abin jira a gani shi ne irin girman kujerun Ministocin da za a bai wa tsoffin gwamnonin.

Saurari rahoton Rukaiya Basha cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:14 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG