Masu Kada Kuri’u Ya Kamata Su Zabi Shugabanni Ba Kotu Ba - Jonathan

CEDEAO- JONATHAN GOODLUCK

Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan ya jadada mahimmancin yin gagarumin gyara a tsarin zabe a Najeriya ya koma tsarin mayar wa masu kada kuri’u ikon da kundin tsarin mulkin kasar ya ba su.

Jonathan ya bayyana katsalandan da bangaren shari’a ke yi a yayin zabuka musamman ayyana nasarar wanda ya ci zabe a matsayin mummunan dabi’a da ya sabawa tsarin mulkin dimokradiyya.

Tsohon shugaba Goodluck Jonathan, ya bayyana hakan ne a matsayin babban bako a wani taron gidauniyar matasa da ya gudana a birnin tarayya Abuja wanda mai gidan talabijan TOS, Ms. Osasu Igbinedion ta shirya.

Goodluck ya ce bangaren siyasar kasar ya fara wuce gona da iri, tare da kara da cewa, yanayin tsarin siyasa a Najeriya da aka dauko ba ya taimakawa wajen barin mata su shiga siyasa a dama da su.

Karin bayani akan: Goodluck Jonathan, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

A cewar shi, tsarin mafi dacewa shi ne a bar hukumomin zabe su na sauke nauyin da ya rataya a wuyansu kacokan tare da barin suna ayyana wanda ya lashe zabe.

Daga karshe, Jonathan ya ce, kasashen da ke gudanar da sahihan zabuka cikin gaskiya da adalci ba sa fuskantar shigar da yawan kararraki bayan zabe ya na mai cewa, yawan shigar da kararraki da ake shigarwa bayan zabuka na daga cikin alamun tsarin mulkin dimokuradiyya mai rauni.