Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yajin Aiki: Majalisar Wakilai Na Shirin Ba Da Umarnin Kama Magatakardar Majalisar Likitocin Najeriya


Nigeria National Assembly
Nigeria National Assembly

Kwamitin majalisar wakilan Najeriya kan ayyukan kula da kiwon lafiya ya yi barazanar ba da umarnin kama magatakardan majalisar likitoci da suka hada da masu kula da hakori ta Nijeriya, Tajudeen Sanusi.

Matakin ya biyo ne bayan da ya ki mutunta gayyatar da kwamitin majalisar wakilai kan kiwon lafiya ya yi masa.

Kwamitin majalisar wakilan dai ya gayyaci Tajudeen Sanusi, ya bayyana a gaban sa a ranar Alhamis don amsa wasu tambayoyi a kan yajin aikin da likitoci ke yi ya zuwa yanzu da kuma biyan hakkokin manyan likitoci.

Tajuddeen Sanusi, Magatakardan majalisar likitocin Nijeriya
Tajuddeen Sanusi, Magatakardan majalisar likitocin Nijeriya

Rashin bayyanar Sanusi a gaban ‘yan majalisar dai ya tilasta dakatar da taron bayan an isar mu su da wasika da ya aika cewa yana halartar wani zaman kotun majalisar likitocin a lokacin da su ke zaman jiran sa.

Shugaban kwamitin, Hon. Tanko Sununu, ya ce Sanusi ya ki mutunta gayyatar da kwamitin ya yi masa kan muhimmin batun da ya shafi kasa a yayin da ya zabi halartar wani taro na kashin kan sa.

A cewar dan majalisar, "mun tura wasikar gayyata ga muhimman masu ruwa da tsaki a sha'anin kiwon lafiya don su halarci zaman don neman mafita da biyan bukatun likitocin da ke yajin aiki, sai dai abun takaici shi ne yadda Sanusi ya ki mutunta gayyatar."

Akan haka ya ce ba zasu zura ido al’umma su cigaba da wahala ba.

Hon. Tanko Sununu, Shugaban Kwamitin majalisar wakilai kan kiwon lafiya
Hon. Tanko Sununu, Shugaban Kwamitin majalisar wakilai kan kiwon lafiya

Sununu, ya ce an rasa rayuka a yayin wannan yajin aiki, an katse ayyuka, an hana mutane samun ingantaccen kiwon lafiya da samun kulawa a asibitoci kuma abun lura shi ne yadda a Najeriya, ‘yan kasa ke biyan kashi 70 cikin 100 na neman kulawa a fannin kiwon lafiya.

Ya kara da cewa tattalin arzikin kasa na cikin matsi, don haka batun kiwon lafiya na kara fuskantar kalu bale, don haka a matsayin su na wakilan al’umma ba za su kyale kasar ta ci gaba haka a haka ba.

XS
SM
MD
LG