Masu Amfani Da Tiktok A Amurka Sun Koma Wata Manhaja Mallakin Kasar China

A bara, Amurka ta zartar da dokar da za ta tilastawa ByteDance kodai ya sayar da dandalin TikTok ko kuma ya rufe shi kan nan da 19 ga watan Janairun da muke ciki.

Sakamakon fusata da yiyuwar gwamnati Amurka ta haramta amfani da dandalin sada zumunta na Tiktok, dimbin masu amfani da dandalin a Amurka sun koma kan wata manhajar mallakin kasar China, inda da dama daga cikin ke wallafa sakon bijirewar dake cewa: “ku tatsi bayanai na!”

Dandalin na Tiktok ya zama wani fagen fama da ke nuna karin zaman tankiya tsakanin Amurka da China, inda gwamnatin Shugaba Joe Biden ke zargin manhajar da baiwa mahukunta birnin Beijing damar tatsar bayanai da yin leken asiri akan masu amfani da ita-zargin da kasar China da mamallaka Tiktok din ByteDance suka musanta.

A bara, Amurka ta zartar da dokar da za ta tilastawa ByteDance kodai ya sayar da dandalin TikTok ko kuma ya rufe shi kan nan da 19 ga watan Janairun da muke ciki.

Sakamakon karatowar da wa’adin yake kara yi, yawan sauke manhajar ‘Xiaohoungshu’, wacce wani nau’i ne na shafin Instagram dake maida hankali akan salon rayuwa kwatankwacin TikTok ya kure mizanin rumbun sauke manhajoji na “Apple Store” a jiya Litinin.

Maudu’in #TikTokRefugee ya samu fiye da mutane miliyan 100 da suka yi tozali da shi da yammacin yau Talata.