Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Wakilan Amurka Ta Zartar Da Kudirin Dokar Da Ka Iya Haramta Amfani Da Manhajar TikTok A Fadin Kasar


Majalisar Wakilan Amurka ta zartar da muhimmin kudirin daka iya haramta amfani da manhajar Tik tok a kasar.

WASHINGTON DC - Dokar zata baiwa katafaren kamfanin sada zumunta na "ByteDance " mallakin kasar China, wa'adin watanni 6 ya sayar da hannayen jarinsa ko kuma a toshe manhajar a fadin Amurka.

An jima 'yan majalisar na nuna damuwa game da tasirin kasar China akan manhajar ta TikTok.

Kamfanin kasar China Bytedance ne ya mallaki manhajar ta TikTok da aka kirkira a shekarar 2012.

An yiwa kamfanin mai mazauni a birnin Beijing rijista ne a tsibirin Cayman, amma yana da ofisoshi a fadin nahiyar turai da Amurka.

Idan har kudirin bai samu sahalewar Majalisar Dattawan Amurka ba, Shugaba Joe Biden yace ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen rattaba masa hannu da zarar ya iso kan teburinsa, abinda ake ganin na iya sabbaba takaddamar diflomasiya da kasar China.

Kamfanin Bytedance na bukatar samun sahalewar jami'an kasar China kafin kammala cefanar da hannayen jarinsa ala tilas, matakin da mahukuntan birnin Beijing suka sha alwashin kalubalanta.

Akwai dokar tsaron China data bukaci kamfanonin kasar suyi musayar bayanai da gwamnati matukar aka bukaci hakan.

Manhajar ta TikTok tayi kokarin baiwa hukumomin dake sanya idanu akan shafukan sada zumunta tabbacin cewar ta dauki matakan kare bayanan mutum milyan 150 dake amfani da ita a Amurka daga ma'aikatan kamfanin Bytedance dake kasar China.

Duk da cewar majalisar nada mambobi daga jam'iyyu guda 2, an zartar da kudirin da kyakkyawan rinjaye, amma duk da haka sai ya samu sahalewar Majalisar Dattawa da sa hannun Shugaban Kasa kafin ya zama doka.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG