A jiya Juma’a wata kotun daukaka kara ta tarayya a birnin Washington na Amurka, ta amince da wata doka da ta bukaci a sayar da fitacciyar manhajar sada zumunta ta TikTok ga wanda ba dan kasar China ba ko kuma a rufe ta baki daya a Amurka nan da wata mai zuwa.
Kotun ta ba da misali da hujjojin da gwamnatin tarayya ta gabatar cewa TikTok na da hatsari ga tsaron kasa.
Hukuncin na iya jefa Amurkawa miliyan 170 da ke amfani da TikTok akai-akai, a cikin halin rashin damar yin amfani da dandalin na sada zumunta da ya sami gagarumin ci gaba a duniya a cikin 'yan shekarun nan.
Hakan kuma na iya nufin cewa miliyoyin Amurkawa da suke ƙirƙirar wallafe-wallafe a TikTok - waɗanda wasunsu ke dogaro da kudin da suke samu ta hanyar wadannan wallafe-wallafen don bukatun rayuwarsu - na iya yankewa daga masu bibiyar su.
Gwamnati ta yi iƙirarin cewa TikTok yana da haɗari na musamman ga tsaron ƙasa saboda yana tattara bayanai masu yawa game da masu amfani da shi, da kuma saboda a ƙarshe gwamnatin China tana da karfin iko kan uwar kamfanin, ByteDance, da kuma tsarin da ke ƙayyade iya abin da masu amfani da TikTok ke iya gani.
Saboda ByteDance yana da mazauni ne a China, yana aiki ne a karkashin dokokin kasar, ciki har da matakan da ke buƙatar kamfanoni masu zaman kansu su yi aiki tare da hukumomin leken asiri na gwamnati.
Alkalai uku na Kotun daukaka karar ta Amurka na gundumar Columbia, sun tabbatar da cewa gwamnati na da sha'awar daukar matakai "don dakile kokarin China na tattara dimbin bayanai game da dubun-dubatar Amurkawa", da kuma" iyakance ikon China na sarrafa bayanai cikin sirri a dandalin na TikTok."
Dandalin Mu Tattauna