Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tiktok Ya Goge Bidiyo Miliyan 2.1 A Najeriya Saboda Saba Ka’idojinsa-Rahoto


Bidiyoyin da al’amarin ya shafa basu kai kaso 1 cikin 100 na abubuwan da aka dora a kan dandalin ba a dan tsakanin da rahoton ya bayyana.

Dandalin sada zumunta na Tiktok ya bayyana cewar ya goge fiye da bidiyo miliyan 2.1 a Najeriya a zango na 2 na 2024 saboda sabawa ka’idojin da ya tsara.

A cewar rahoton aiwatar da ka’idojin da ya wallafa a jiya Talata, Tiktok yace matakin wani bangare ne na kokarin da kamfani yake yi na inganta tsaftace harkokinsa tare da samar da dandalin da zai zama maras hatsari ga masu amfani da shi.

“Bincike ya nuna cewar an goge kaso 99.1 cikin 100 na irin wadannan bidiyo kafin masu amfani da dandalin su kai korafi a kansu, inda aka goge kaso 90.7 cikin 100 na bidiyon cikin sa’o’i 24.

"Alkaluman sun nuna jajircewar Tiktok wajen kaucewa abubawan daka iya cutarwa, tare da kawar da dukkanin wani abu mai hatsari ga masu amfani da dandalin a Najeriya,” a cewar rahoton.

Bidiyoyin da al’amarin ya shafa basu kai kaso 1 cikin 100 na abubuwan da aka dora a kan dandalin ba a dan tsakanin da rahoton ya bayyana.

Tiktok yace ya gode fiye da bidiyo milyan 178 a fadin duniya a watan Yunin 2024, inda naura da aka tsara ce da kanta ta goge bidiyo milyan 144 daga cikinsu.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG