Masana kimiyyar siyasa na hasashen cewa tsige Shugaba Donald Trump da Majalisar Wakilan Amurka ta yi ba zai taba mutuncin dimokradiyyar Amurka a idon duniya ba, musamman kasashe masu tasowa.
Masanan na cewa ko yanda ba a samu bude wuta a mamaye Majalisar Dokokin ba da kuma nasarar tsigewar a Majalsar Wakilai, wani sabon salo ne da jami'an tsaro da 'yan siyasar kasashe da ke koyi da manyan kasashen dimokradiyya za su yi.
Za a cigaba da tunawa da Trump kan yanda ya kan furta da aikata asalin abun da ya ke cikin zuciyarsa ko da a ganin wasu hakan zai taba mutuncin Amurka a tsakanin kasashen duniya.
Duk da haka masanin kimiyyar siyasa a Jami'ar Abuja, Dr.Farouk BB Farouk ya ce da dai mamaye Majalisar Amurka da magoya bayan Trump su ka yi, ya auku a Najeriya ne da labari ya sha bamban.
Babban dan siyasar APC mai mulki a Najeriya, Alhaji Kabiru Giant, ya ce yanzu ya dace kowace kasa dabarar ta ta fissheta a dimokradiyya, ganin abin da ya faru.
Masanan na cewa za a tuna Trump a matsayin Shugaba da ba lallai sai da taimakon jami'in labaru ba wajen fitar da labarunsa, don ya kan rubuta duk abin da ya ke son duniya ta sani ta shafinsa na twitter mai fiye da mabiya miliyan 88.
Hatta Shugaba mai jiran gado Joe Biden bai ko kama kafar Trump a mabiya na twitter ba don ko a lokacin zaben da Biden ya lashe, Biden ba shi da mabiya da su ka haura miliyan goma sha daya. Yanzu sun kai sama da miliyan 23 don albarkacin nasarar da ya samu.
Ga Nasiru Adamu Elhikaya da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5