Wannan karon, ba kamar yadda ya kasance a baya ba, wasu ‘yan jami’iyar Republican ta Shugaban kasa sun bayyana goyon bayansu ga wannan mataki na tsige Shugaban wanda a baya suka kalubalanci yunkurin da ‘yan Democrat suka yi na tsige Trump bisa zargin amfani da matsayin sat a yanda bai dace ba.
Wasu kafafen labarai sun ce Sanata Mitch McConnell daga jihar Kentucky, shugaban ‘yan Republican a Majalisar Dattawa, ya fada wa takwarorinsa cewa ya amince shugaba Trump ya aikata laifin da ya cancanci a sauke shi daga shugabancin kasar, kana ya yi na’am da yunkurin Democrat na tsige shugaban kasar.
A yau ne dai Majalisar Wakilai ke kada kuri’a domin tabbatar da tuhuma a hukumance a kan shugaba Trump na ingiza magoya bayan sa su tada tarzoma a kan kasar.
Mallam Hassan Sallau Jibiya, dan Najeriya mazaunin Amurka, kuma mai sharhi ne a kan siyasar Amurka, ya yi hasashe cewa za a ga ‘yan jam’iyyar Republican da dama da zasu bada goyon baya ga tsige shugaban kasa, haka zalika akwai yiwuwar aiwatar da wannan shiri cikin gaggawa ba kamar yanda aka gani a baya ba.
Jibiya ya kwatanta tarzomar ta ranar Laraba da abin kunya da alhini da Amurka ta gani cikin sama da shekaru 200, bayan da sojojin wata kasa(Birtaniya) suka abka wa ginin majalisar dokokin Amurka har ma suka kona majalisar. Ya ce tarzomar ta tada ma duk wani ba-Amurke mai kishin kasa hankali.
Hassan Jibiya ya ce yunkurin tsige shugaba Trump da su sharhi suke masa kallon na bai daya da majlisar Amurka za ta yi, alama ce dake tabbatar da dimokaradiyar Amurka ta fi karfin mutum daya kuma ba a nuna bangaranci ko siyasar ido-rufe a kasar.
Duk da cewar ana kallon ‘yan jami’iyar Trump suna mara masa baya amma wannan karo sun nuna akwai layi da suka ja da ba zasu yarda ya wuce wannan layi ba.
Ga dai tattaunawar Sashen Hausa da Hassan Sallau Jibiya: