'Yan Democrat suke da rinjaye a majalisar kuma su na da isassun kuri’un da za su amince a tsige shugaban, amma yanzu ana samun karin 'yan Republican da ke goyon bayan kudurin.
'Yar majalisa Jaime Herrera Beutler ta sanar a yammacin jiya Talata cewa za ta kada kuri’ar goyon bayan tsige shugaban, ta fada a wata sanarwa cewa Trump ya saba alkawarin da ya dauka a matsayin shugaban kasa.
'Yar majalisar wakilai Liz Cheney, kuma daya daga cikin shugabannin 'yan Republican a majalisar wakilai, da ta ke bayyana goyon bayanta akan tsige shugaban, ta ce ba a taba samun cin amanar da shugaban kasa ya yi ba kamar wannan.
Shi dai shugaba Trump ya fito ya yi Allah wadai da zanga-zangar ta majalisar dokoki, ya kuma nesanta kansa daga wadanda suka gudanar da ita.