Kungiyar Ansaru dai tafi mayar da hankaline wajen yin garkuwa ga ‘yan kasashen waje don neman kudin fansa, abinda ya kai ga Amurka tasa tukwicin kudi har Dala Miliyan Biyar ga duk wanda ya bayar da labarin da zai taimaka a cafke shi.
Hedikwatar tsaron Najeriya ta bayyana cafke Khalid Al Barnawee a jihar Kogi, to kome hakan ke nufi ga sha’anin tsaron kasar? Tsohon kwamandan mayakan sama Ahmed Tijjani baba Gamawa, yace “kama wannan mutumin na nuna cewa insha Allahu, karshen wadannan mutane yazo karshe, abune da aka ce Amurka da sauran kasashe na nemansa har ma suka sa kudin tukwici kansa Allah ya baiwa dakarun Najeriya nasara har suka kama shi, saboda haka ina tabbatarwa da mutane insha Allahu karshensu yazo kenan.”
Shima tsohon jami’in leken asirin sojan Najeriya, Aliko El-Rashid Harun yace ba lalle bane damke Al Barnawee ya canza al’amurra, inda yace irin su Al Barnawee wani bangare ne na Boko Haram, kuma kamar yadda ake a fadin duniya duk lokacin da aka kama shugaba yana dan dakatawa na wasu yan kwanaki wani zai maye gurbin sa.
Tunda yanzu an cafke Al Barnawi ko menene abinyi yanzu, mun tuntubi tsohon hafsan sojan kasa Kanal Aminu Isah Kwantagora, wanda yace “Dokokin kasa da kasa su za a duba, tunda Najeriya na nemansa su hukuntashi kafin a mikawa Amurka shi suma su hukuntashi.”
Your browser doesn’t support HTML5