Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojan Najeriya Ta Dauki Mataki Kan Wasu Hafsoshin Soji


Wata tankar sojan Najeriya tana sintiri a cikin garin Mubi Jihar Adamawa bayan da aka kwace garin daga hannun 'yan Boko Haram
Wata tankar sojan Najeriya tana sintiri a cikin garin Mubi Jihar Adamawa bayan da aka kwace garin daga hannun 'yan Boko Haram

Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da sallamar Janal Aliyu Momoh, kwamandan sojojin da suka saka ido a zabukan Ekiti da Osun da wasu manyan Hasoshin Soji 3 da ake zargin sunyi anfani da karfi da kuma kudi wajen tauyewa masu zabe hakkinsu.

Daukar matakin sallamar ya biyo bayan wani bincike da rundunar sojan Najeriya ta gudanar, game da rawar da sojoji suka taka a zaben da akayi a jihohin Osun da Ekiti da kuma zaben shugaban kasa a aka gudanar a shekarar da ta gabata.

Haka kuma rahotanni sun bayyana cewa akwai wasu sojoji guda 12 da yanzu haka aka mika su ga hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa EFCC, domin gudanar da binciken zarginsu da akeyi na karbar na Goro daga hannun wasu manyan yan siyasa kasar a wancan zaben da aka gudanar.

Daga cikin sojojin akwai Majo Janal guda 3 da kuma wasu Burgediya Janal guda 3 da hafsoshi masu mukamin Kanal guda 4 da kuma Laftanal Kanal guda 1.

Kakakin rudunar sojan Najeriya, kanal Sani Usman Kuka Sheka, shine ya tabbatar da daukan wannan mataki akan hafsoshin sojan, ya kuma ce an tura Kaftin Sagir Koli jami’in asirin sojin nan da ya fallasa wannan abin kunya a wancan lokaci, domin karo karatu a wata kasa ta katare.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG