Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bamu Hana Shigowa Da Shinkafa Kwata Kwata Ba


A wata tattaunawa ta musammam da Mallam Garba Shehu mai baiwa shugaban kasar Najeriya shawara kan harkokin da suka shafi yada labarai, Mallam Garba yayiwa Muryar Amurka karin haske kan batun shigowa da shinkafa daga kasashen waje zuwa kasar.

Duk da yake dai farashin Shinkafa yanzu a Najeriya ya ninka yadda yake a baya, inda wasu ke ganin cewa rashin noman Shinkafar da zata wadaci kasar, haka kuma an hana shigowa da Shinkafa cikin Najeriya haka yasa farashinta yayi tashin gwauran zabi. A yayin da yake karin haske kan wannan batun Mallam Garba yace a iya saninsa gwamnatin Najeriya bata hana shigowa da Shinkafa kwata kwata ba daga kasashen waje.

Gwamantin Najeriya ta haramta shigowa da shinkafa takan iyakokin Najeriya, amma bata teku ba, domin hanyar Teku itace hanya kadai da gwamnatin Najeriya ta amincewa duk wasu manoma da yan kasuwa su shigo da kayan abinci musammam ma shinkafa. Kasancewar a tashoshin jiragen ruwa dake bakin Teku nan ne ma’aikatan Kwastam da na kula da lafiya suke.

Shigowa da shinkafa ta kan iyakokin Najeriya, kamar shigowa da kayan ta kasar Nijar ko Kamaru da dai sauran makwabta na kawo matsala ga gwamnatin Najeriya, domin babu ma’aikatan da ya kamata ace sun duba kayan sun kuma karbi harajin da ya kamata gwamnatin Najeriya ta karba.

Mallam Garba Shehu dai yace maganar gwamnatin Najeriya ta haramta shigowa da Shinkafa cikin kasar ba haka yake ba, ga duk mai son shigowa da shinkafa Najeriya tabbas sai dai ya shigo da ita ta bakin teku kamar yadda gwamnati ta tsara.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:49 0:00

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG