Domin gani an yaki cutar zika yanzu haka dai masana daga sassa daban-daban na duniya da suka hada da kwararru a bincike, malaman ilimin kiwon lafiya, hukumomi masu bada gudun mowa a harkan kiwon lafiya kowannen su yayi alkawarin zai bada bayanan da ya samu domin ayi musayar ra'ayi sabo da shawo kan wannan cutar.
Wannan yarjeniyar ya samu sa hannun kungiyoyi har sama da 30, kuma ko wannen su yayi alkawarin cewa zai mikawa dan uwansa duk wani bayanin da ya samu ko ya gano game da wannan cutar domi ganin an samu nasarar yaki da ita.
Wasu daga cikin kungiyoyin ko sun hada da kungiyar likitocin masu bada agajin gaggawa kyauta wadanda da turanci ake kira Doctors without Borders, hukumar Bill and Milinda Gate, kungiyar masu dakunan bincike na jama'a wato Public Library of Science, sai cibiyar yaki da cututtuka da kare su na Amurka, da takwarar ta na kasar China.
Sauran ko sune Journal od the American MedicalAssotion, sai Network and US INSTITUTE NATIONAL da dai sauran su dukkan wadannan sun amince suyi musayar bayanai domin ganin an shawo kan wannan cutar.