Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Jiragen Kasa Biyu Sunyi Karon Batta A Jamus


Karon battar wasu jiragen kasa biyu.
Karon battar wasu jiragen kasa biyu.

Jami’an ceto a kasar Jamus suna amfani da jirage masu saukar Ungulu da kananan jiragen ruwa wajen ceto dimbin mutane Fasinjojin da wani hatsarin jirgin kasa da ya yi karo a wani bangaren karkara na Kudancin kasar.

Hukumomin kasar sun bayyana akalla mutuwar mutane 10 da kuma jikkatar wasu fasinjojin a yau, lokacin da jiragen kasa guda biyu suka yi taho mu gama da juna, a lokacin kuma kowane jirgin yana kan gudun Kilomita 100 a cikin sa’a guda.

Wannan mummunan karon jiragen ya faru ne a daidai inda bari daya kogi ne daya bangaren kuma kungurmin daji ne, wanda hakan ya kawo cikas ga isar motocin kai dauki wajen cikin gaggawa.

Jami’an ‘yan sanda sun ce an kera jiragen da wani irin salon cin Birkin karfi da yaji don gujewa irin wannan hadari, wanda hakan ta sa sun dukufa binciken musabbabin mummunar wannan karon battar jiragen.

XS
SM
MD
LG