Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ashe Gawayi Na Maganin Cututukan Da Kan Addabi Fatar Mutun


Mutane da dama kanyi amfani da gawayi wajen wanke hakoran su, haka kuma sukan samu natsuwar cewar yana musu aiki da ya kamata. Dr. Jessica Wu, likitar fata a Los Angeles, ta kasar Amurka, ta bayyanar da cewar lallai gawayi, na da matukar amfani ga lafiyar fatar jikin mutun.

Duk dai da cewar babu wani binciken kimiyya da ya bayyanar da cewar, gawayi magani ne ga fata. Amma abun da tasani ne cewar, mafi akasarin magungunan fata, ko da kuwa na gyaran jiki ne, suna dauke da sunadarin da aka fitar da su daga gawayi. Don haka gawayi yana dauke da wasu sinadarai da suke taimaka ma fata, koda kuwa a lokacin da fatar ke dauke da wasu abubuwa ne da zasu cutar da ita.

Labari mai dadi a nan shine, babu ta yadda za’ayi mai amfani da sinadaran da suke dauke da gawayi, ko amfani da shi gawayin kanshi, su kamu da cutar da lafiyar fatar zata raunana. Hasali ma sai dai su taimaka ma mutun wajen samun nagartacciyar lafiya. Idan ma mutun na dauke da wasu kwayoyin cututuka a fatar jikin shi, to amfani da mai ko ruwan goge fata masu dauke da sinadaran gawayi, zasu taimaka ba shakka wajen gyaran fata da samun lafiya akowane lokaci. Tun da dai ya bayyana babu wani cutarwa ko lahani da gawayi ya ke yima fata, to hakan na nuni da cewar zai taiamaka ma fata kenan.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG