Hukumar lafiya ta duniya wato WHO tace kar jami'an kiwon lafiya su yadda su rika karban gudun mowar jinin mutanen da suka dawo daga kasashen da cutar Zika ta bulla.
Cutar wanda keda nasaba da cizon sauro ya bazu ne a kasashen dake yankin Latin Amurka, musammam Brazil.
An bayyana cutar dai tana matukar illa ga mata masu juna biyu.
Hukumar ta lafiya ta fadawa kanfanin dillacin labarai na Faransa cewa yanzu haka daga cikin watan oktoba kawo yanzu an samu masu dauke da cutar da suka kai har dubu 4 a kasar Brazil.
Sai dai masana sunce suna mamakin yadda aka yi cutar bata bayyana ba a wasu sassan kasashen dake yankin na Latin Amurka inda cutar tayi Kamari.
Sai dai kasar Spain ta bayyana jiya cewa an samu kwayar cutar a jikin wata mata mai ciki wadda ta tafi Colonbia, wannan dai shine karo na farko da aka samu cutar a wata kasar turai.
Yanzu haka dai ba maganin wannan cutar aduk duniya sai dai masana ilmin magunguna suna nan suna aiki ba dare ba rana domin samar da maganin.