Miliyoyin ‘yan mata da mata ne yanzu haka ke ci gaba da fuskantar kaciyar da akeyi wa mata fiye da yadda ake yi musu ada.
Hukumar kula da yara ta Majalisar Dinkin Duniya ne wato UNICEF ta bayyana hakan.
A cikin wani rahoton da hukumar ta fitar tace akalla mata da yawan su yakai miliyan dari 2 suka samu kansu cikin wannan halin, kuma kusan rabin wannan adadin sun fito ne daga kasashe uku kacal wato Masar, Habasha, da Indonisiya.
Alkalummar baya-baya nan ya bayyana cewa kusan ‘yan mata da mata miliyan 70 aka kiyasta aka yiwa wannan kaciyar a shekarar 2014, kafin adadin ya haura sailin da aka samu kari daga kasar Indonisiya, inda aka hana wannan kaciyar tun a shekarar 2006.
Kasar Somalia ita ce tafi yawan matan da akayi wa wannan kaciya domin an kiyasta kashi 98 na ‘yan matan da shekarun su yake tsakanin 15 zuwa 49 suna da wannan abu a jikin su.
Suma kasashen Guinea, Djibouti, da Saliyo adadi ya haura yadda aka sani ada.
Gaba daya a kasashen duniya inda ake wannan abu ‘yan mata dake da shekaru 14 ko kasa da haka anyi wa mata har miliyan 44 wannan kaciya.