Manyan Masu Tsaron Ragar Ghana Ba Za Su Je Qatar Ba

Tawagar 'yan wasan Ghana

Hakan na nufin ya zama dole Ghana ta dauki Lawrence Ati-Zigi wanda shi ne zabinta na uku a matsayin mai tsaron raga.

Tawagar kwallon kafar kasar Ghana za ta je gasar cin kofin duniya a Qatar ba tare da manyan masu tsaron ragarta biyu ba, saboda rauni da suka ji.

Mai tsaron ragar Ghana, Jojo Wollcott wanda shi ne zabinta na farko ya karya dan yatsansa gabanin wata karawa da kungiyarsa ta Charlton ta yi a Ingila a karshen makon da ya gabata.

Shi kuma Richard Ofori, wanda shi ne zabinta na biyu, ya ji rauni a kwaurinsa.

Hakan na nufin ya zama dole Ghana ta dauki Lawrence Ati-Zigi wanda shi ne zabinta na uku a matsayin mai tsaron raga.

Sauran masu tsaron ragar biyu da aka dauka don marawa Ati-Zigi baya sun hada da Abdul Manaf Nurudeen da Ibrahim Danlad mai shekaru 19.