Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Da Ghana Sun Tashi Canjaras, Egypt Ta Ci Senegal 1-0


Wasan Najeriya da Ghana
Wasan Najeriya da Ghana

A dai ranar Talata, 29 ga watan Maris kasashen biyu, wadanda makwabtan juna ne a yankin yammacin Afirka, za su sake haduwa a Abuja, babban birnin Najeriya.

Najeriya da Ghana sun tashi babu ci a wasan da suka kara don neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar a bana.

Kasashen biyu wadanda suke da jikakkiyar hamayya a tsakaninsu a fagen kwallon kafa, sun kwashe minti 90 ba tare da wani ya zura kwallo a raga ba.

Bangarorin biyu dai sun yi ta kai wa juna hare-hare, ko da yake, kididdiga ta nuna cewa ‘yan wasan Black Stars sun fi Super Eagles rike kwallo a wasan wanda aka buga a birnin Kumasi.

‘Yan wasan Najeriya sun yi ikirarin samun bugun fenariti bayan da mai tsaron bayan Ghana ya fadi akan kwallo.

Amma bayan duba akwatin VAR da ke tantance ainihin abin da ya faru, alkalin wasan ya ce babu fenariti.

A dai ranar Talata, 29 ga watan Maris kasashen biyu, wadanda makwabtan juna ne a yankin yammacin Afirka, za su sake haduwa a Abuja, babban birnin Najeriya.

Wasan na ranar Talata, shi zai fayyace kasar da za ta je gasar cin kofin duniyar a tsakanin kasashen biyu.

Sau shida Najeriya na zuwa gasar ta cin kofin duniya yayin da ita kuma Ghana ta je gasar sau uku, har ta taba kai wa zagayen quater-finals a shekarar 2010.

Sau uku Najeriya na zuwa zagayen ‘yan 16 a gasar ta cin kofin duniya.

Egypt 1 Senegal 0

A daya wasan kuma da aka buga tsakanin Egypt da Senegal, ‘yan wasan na Masar sun doke Senegal da ci 1-0.

A minti na hudu, Senegal ta ci gida bayan da kwallon ta doki kafar mai tsaron bayan Senegal Saliou Ciss ta fada raga bayan da Mohamed Salah ya doko kwallon.

Senegal ce ta bi Egypt gida a wannan wasa na farko.

Wannan wasan tamkar maimaicin wasan karshe ne da aka buga a watan Fabrairu a gasar cin kofin nahiyar Afirka, inda Senegal ta doke Egypt da ci 4-2 a bugun fenariti.

A mako mai zuwa Egypt za Senegal Dakar domin buga wasan karshe da zai fayyace kasar da za ta je gasar ta cin kofin duniya.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG