‘Yan wasan Ghana Black Stars sun kafa sansaninsu a Doha, babban birnin Qatar gabanin fara gasar cin kofin nahiyar Afirka.
A ranar 9 ga watan Janairun 2022 za a bude gasar a kasar Kamaru da ke karbar bakuncin gasar
Kasashe 24 ne za su fafata don neman lashe kofin.
Hukumar kwallon kafar kasar ta Ghana ta ce ya zuwa ranar Litinin ‘yan wasa kasar sun fara hallara a sansanin.
“‘Yan wasan da suka shiga sansanin sun hada da Richard Atta, Lawrence Ati Zigi, Alexander Djiku, Mubarak Wakaso, David Abagna, Daniel Kofi Kyereh.
Sauran sun hada da, “Gideon Mensah, Abdul Fatawu Issahaku, da Maxwell Abbey Quaye.” In ji hukumar kwallon kafa ta Ghana.
Ghana na rukunin C, da ke dauke da Morocco, Gabon da kuma Comoros.
A ranar bakwai ga watan Janairu ‘yan wasan na Black Stars za su isa kasar ta Kamaru.
Za ta fara wasanta na farko da Morocco a gasar wacce za a kammala a ranar 6 ga watan Fabrairu.