Manyan Jami'an Amurka 2 Zasu Bada Shaida A Bainar Jama'a

Wasu manyan jami'an Amurka biyu za su ba da shaida a bainar jama'a kan ko akwai kanshin gaskiya ko a'a game da zargin nan mai sarkakkiya, amma kuma mara hujja, wanda Shugaban Amurka Donald Trump ya yi na cewa tsohon Shugaba Barack Obama ya tatsi bayanai a hedikwatar Trump Tower

Da Shugaban Hukumar Bincike Ta FBI James Comey, da Shugaban Hukumar Tsaron Kasa Admiral Michael Rogers, za su iya sani idan an yi tatsar bayanan. Za su ba da ba'asi gaban Kwanitin Bayanan Sirri Na Majalisar Wakilan Amurka.

Har tsawon makonni biyu Trump ya zake kan wannan zargin, Koma bayan da jerin jami'ai, ciki har da Kakakin Majalisar Wakilai Paul Ryan, da manyan 'yan Republican da Democrats, na Kwamitocin Bayanan Sirri na Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai, sun ce babu wata shaidar da ta tabbatar da zargin da Trump, ya fara yi tun daga ranar 4 ga watan Maris a jerin sakonni ta kafar sadarwar twitter.

Jiya Lahadi dan jam'iyyar Republican a Majalisar Tarayya Devin Nunes, wanda shi ne ma Ciyaman din Kwamitin bincike na Majalisar Wakilai ya gaya ma kafar labarai ta Fox News, cewa ko ma sabbin bayanan da su ka samu ranar Jumma'a daga Ma'aikatar Shari'a game da wannan zargin ba su sa ya sauya ra'ayi ba.