Koriya Ta Arewa ta gwada wani katafaren injin din cilla roka daga kasa, a cewar kafar labaran gwamnatin kasar ta KCNA a yau dinna Lahadi.
Shugaban Koriya Ta Arewar Kim Jong Un ya ce an yi nasara a wannan gwajin, sannan ya "jaddada cewa kwanan nan duniya za ta ga irin gagarumar nasara mai kafa tarihi, wadda mu ka yi yau," a cewar kafar ta KCNA.
Wannan gwajin ya kunshi harba injin din rokar yayin da ya ke bisa wata marika a kasa, ba tare da harba wani makami mai linzami ba. An yi wannan izawar ce a tashar harba roka ta Tongchang-ri, daura da iyakar Koriya Ta Arewar da China, a cewar kafar ta KCNA, wadda ta ce Kim Jong Un ya je tashar da asuba, ya kafa tabaron hangen nesa sannan ya bayar da umurnin fara gwajin.
Tuni dai Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson, wanda ke ziyarar aiki a karon farko a Nahiyar Asiya, tun bayan zamansa Sakataren, ya yi kiran da a bullo da wata sabuwar hanyar tinkarar karuwar barazanar nukiliya daga Koriya Ta Arewa.