Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Syriya Da 'Yan Tawaye Sun Fafata A Birnin Damascus


Sojojin Siriya da dakarun 'yan tawaye sun fafata a sassan birnin Damascus jiya Lahadi, bayan da 'yan tawayen su ka kutsa cikin babban birnin kasar ta wata hanyar karkashin kasa a cikin dare su ka kai hare-haren bazata a wuraren da ke hannun gwamnati a birnin.

'Yan tawayen sun fara ne da kai hare-haren bam da wasu motoci biyu da kuma wasu jerin hare-haren kunar bakin wake, a cewar kungiyar kare hakkin dan adam a Siriya mai hedikwata a Burtaniya.

'Yan tawayen sun kwace gine-gine da dama a unguwar Jobar, a wannan birnin mai cike da matakan tsaro, inda ke da tazarar kilomita biyu a arewa maso gabashin tsohuwar ganuwar birnin, inda har mazauna wurin ke cewa albarusan atilare da rokoki sun yi ta fadawa cikin tsakiyar birnin.

To amma, a cewar kungiyar rajin, bayan dannawar farko da 'yan tawayen su ka yi, sai jiragen yaki na gwamnati su ka yi da'ira a wuraren da 'yan tawayen su ka ja daga su ka yi masu luguden wuta har sau 30, wanda wannan ne al'amari na baya-bayan nan a wannan tashin hankalin da aka kwashe shekaru 6 ana yi.

Facebook Forum

Kudurin wasu 'yan Najeriya na sabuwar shekara a fannin lafiya, da wasu sauye-sauyen da suke fatan yi don samun nasara a rayuwarsu
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 1080p

No media source currently available

0:00 5:16 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 1080p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Karo na biyu kenan a Nijar ake gudanar da bukukuwan Kirsimetin karkashin mulkin soja, inda a bara takunkumin ECOWAS ya dakushe farin cikin
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:52 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG