Sakataren ya ce duk kuwa da kasa jimma matsaya da Ministocin su ka yi, kan batun watsi da tsarin tattalin arzikin nan, na kare kasuwar kayayyakin cikin gida.
"Zan bar wannan wurin da cikakken karfin giwar cewa da ni da takwarorin aiki na, za mu iya aiki tare don inganta tattalin arzikin duniya ta yadda za a cimma tsayayyen tsarin cinakayya," a cewarsa.
Mnuchin, wanda ya yi nuni da kudurin Shugaban Amurka Donald Trump, na taimaka ma kamfanonin Amurka da kuma ma'aikata, ya yi adawa da yinkurin saka batun hana kare kasuwar kayakin cikin gida, a takardar hadin gwiwa ta sanarwar bayan babban taron.
To saidai Mnuchin ya ce har yanzu Amurka na na'am da tsarin kasuwancin nan na iya-ruwa fidda kai.
"Mu na masu na'am da tsarin nan na barin kasuwa ta daidaita kanta, mu na daya daga cikin kasuwanni mafiya girma a duniya, kuma mu na daya daga cikin abokan cinakayya mafiya girma a duniya," a cewar Mnuchin, wanda ya kara da cewa, "duk da fadin haka da na yi, mu na son mu sake nazarin wasu yarjajjeniyoyi," inda ya ke magana takamaimai kan yarjajjeniyar NAFTA.
Facebook Forum