Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Shige Da Fice Zasu Iya Mamaya A Wajan Bikin Kalankuwar


Birnin Philadelphia da ke gabashin Amurka ta fasa yin bikin da ake gudanarwa duk shekara na murnar Cinco de Mayo, bikin da ke jan hankulan mutane fiye da 15,000.

Daya daga cikin masu shirya bikin Edgar Ramirez yace gaba dayan masu shirya bikin sun hadu akan abin bai musu dadi ba amma shine abinda ya kamata ace sunyi, saboda yanayin da ake ciki kan lamarin da ya shafi Al'ummar da suke bakin haure.

Ramirez yace masu shirya bikin suna jin tsoron ma’aikatan kula da baki na gwamnatin tarayya zasu iya zuwa mamaya a wajen bikin kalankuwar a Philadelphia - Birni na biyar mafi girma a fadin Amurka.

Shugaban kasa Donald Trump yayi kira ga jami’an kula da bakin da kuma jami’an fasa kwauri da su kara kwazo wajen kame da kuma mayar da mutanen da suke zaune a Amurka bada iziniba a Amurka.

Cinco de Mayo Ko kuma 5 ga watan Mayu bikine da ake tunawa da nasarar Sojojin kasar Mexico ta shekarar 1862 akan Faransa a yakin Puebla a lokacin yakin Faransa da Mexico. A Amurka , Cinco de Mayo ya canza inda ya zama bikin nuna al’adun da Gadon mutanen Mexico, musanman a wuraren da Yan kasar Mexico suke da yawa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG